SORAH ALQASAS
SURAH QASAS/سورةالقصص
Chapter 28Verse56.
بسم الله الرحمن الرحيم
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinqai.
إِنَّكَ لَا تَهْدِي مَنْ أَحْبَبْتَ وَلَكِنَّ اللَّهَ يَهْدِي مَنْ يَشَاءُ وَهُوَ أَعْلَمُ بِالْمُهْتَدِينَ
MA'ANA:
Lalle ne kai (ya Rasulullahi) ba ka (Iya) shiryar da wanda ka so (Acikin mutane) amma kuma Allah Yana shiryar da wanda Yake so (A mutane) kuma Shi ne Mafi sani daga masu shiryuwa (ai shine mafi sanin suwaye Shiryayyu Na Gaskiya A mutane)
Wanda suka bada Gaskiya da Allah da Manzon shi Bil haqqi kuma suna kyautata ayyukansu Bilhaqqi da Gaskiya.
Yazo ciki Hadisin Annabi SAW cewa" Baffan Annabi SAW ya kasance baya daga cikin wa'yanda suka miqa wuya wato suka karbi musulunci, Sai Annabi Muhammad SAW ya nuna damuwa ga irin halinda baffanshi zai shiga Idan Ya mutu bai karbi musulunci ba.
Shine ubangiji Allah maliccin sama da Qasa ya Aiko Mala'ika jibril da wannan Ayar ta Al-qur'ani cewa agayawa Annabi Muhammad SAW cewa"Shifa Annabi ne Kuma Mai isar da sako" saboda haka Shi bashiba Ikon shiryar da Wanda yakeso amutane saide Allah ne kadai yake da Ikon shiryar da Wanda ya so.
Yazo acikin wani Hadisin Qudusi Na Annabi Muhammad SAW Ubangiji Yana cewa" Ya ku bayina dukkan ku batattune Saide Wanda Na shiryar dashi daga cikin ku, saboda haka Ku nemi Shiriya ta Ni kuma Inshiryar daku"
Allah ka shiryar da mu Hanyar ka madedeciya hanyarka da salihan Bayinka suke Akan ta ka karemu daga fizga Na shaidan aljani ko Mutum ka karemu daga azabar wuta ka Sanya mu cikin Aljannar madaukakiya.
WALLAHU A'ALAM.
Fb page/ROSHANALI134
Comments
Post a Comment